A ran 16 ga wata bi da bi ne Sinawan da ke zaune a ketare suka nuna goyon baya ga dokar hana ballewa daga kasa da aka zatas kwanan baya a gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin.
Wakilan Sinawan da ke zaune a Washington DC na kasar Japan sun yi taron fadin albarkacin bakinsu, inda dukkansu suka bayyana cewa, dokar hana ballewa daga kasa tana ba da taimako wajen yaki da rukunin 'yan neman 'yancin Taiwan da ayyukansu. Haka nan kuma za ta ba da taimako kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da na karko da kuma bunkasuwa a yankin Asiya na tekun Pacific.
A wannan rana kuma a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu, kungiyar duk Afirka ta ingiza kokarin neman dinkuwar kasar Sin cikin lumana ta wallafa wata talla a kan Jaridar Sinawan dake kasar Afirka ta Kudu, inda ta bayyana cikakken goyon baya ga dokar hana ballewa daga kasa da aka zartas a gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin kwanan baya. (Sanusi Chen)
|