A ran 16 ga wata,jaridar `People`s Daily` ta kasar Sin ta buga wani bayani,inda aka bayyana cewa,dokar hana ballewa daga kasa da majalisar wakilan jama`ar kasar Sin ta zartas ita ce dokar dayantaka cikin lumana,kuma ita ce doka ta kare moriyar `yan uwanmu na Taiwan da kuma doka mai yaki da `yancin kan Taiwan.
Bayanin yana nuna cewa,dokar hana ballewa daga kasa tana da muhimmiyar ma`ana wato ta nuna mana matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka sosai,ita ma ta nuna mana imani da niyya na dukkan jama`ar kasar Sin kan batun Taiwan wato suna nacewa ga kiyaye ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasa.
A sa`i daya kuma,bayanin ya yi nuni da cewa,dalilin da ya sa aka tsara dokar nan shi ne don kiyaye moriyar `yan uwanmu na Taiwan.Bayanin ya bayyana cewa,ana fatan dukkan jama`ar kasar Sin wadda ke kumshe da `yan uwanm na Taiwan su gane ma`anar wannan doka daga dukkan fannoni.(Jamila Zhou)
|