A ran 14 ga wata ta hanyoyi daban-dabam ne Sinawan ketare suka nuna maraba da goyon baya ga dokar hana ballewa daga kasa da aka zartas a gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a ran 14 ga wata.
Tarayyar kungiyoyin Amurka ta ingiza ayyukan dinkuwar kasar Sin cikin lumana ta bayar da sanarwa, inda ta ce, an zartas da dokar hana ballewa daga kasa a kasar Sin wani sabon mataki ne da zai shafi tarihi mai zuwa a kan aikin yaki da yunkurin neman 'yancin Taiwan kuma neman dinkuwar kasar Sin.
Sinawan da ke da zama a Canada suna ganin cewa, cikin daidai lokaci kuma abu ne da ya wajaba a tsara wannan dokar hana ballewa daga kasa a kasar Sin. Wannan doka za ta zama tushen doka wajen yaki da rukunin 'yan neman yancin Taiwan da kuma dinke duk kasar Sin cikin lumana.
Ban da wadannan, Sinawa wadanda suke da zama a Austria da Australia da Faransa da Kenya da Japan da kuma sauran kasashen duniya sun kuma nuna maraba da goyon baya ga dokar hana ballewa daga kasa. (Sanusi Chen)
|