Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-14 17:38:58    
Sinawa 'yan kaka gida dake kasar Brazil sun yi babban taro don nuna goyon bayansu ga dokar hana ballewa daga kasa

cri
Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya aiko mana ya bayyana cewa,a ran l3 ga watan nan da muke ciki,a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, kungiyar neman dinke mahaifa ta hanyar lumana ta kasar Sin dake kasar Brazil ta shirya babban taro don nuna goyon bayansu ga dokar hana ballewa daga kasa, wakilai na Sinawa 'yan kaka gida dake kasar Brazil da wakilai na gwamnatin shiyyar Rio kusan 200 sun halarci wannan babban taro.

A gun wannan taro, shugaban wannan kungiyar nan ta bayyana cewa, tsara dokar hana ballewa daga kasa tana dacewa da gudanawar tarihi, kuma ita take wakiltar burin dukkan mutane na kasar Sin, sabo da haka babbar kungiyar nan ta nuna cikakken goyon bayanta ga wannan dokar.(Dije)