Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya kawo mana ya bayyana cewa, a ran l4 ga watan nan da muke ciki, a nan birnin Beijing, a gun taron gana da maneman labarun da ya shirya ya bayyana cewa, matsalar Taiwan harkokin gida na kasar Sin ne, kuma kasar Sin ta hana shishirin waje da za a kai wa matsalar Taiwan, kuma ba mu ji tsoron waje da za a kai mana ba ko kadan.
A lokacin da Mr.Wen Jiabao yake ba da amsa ga tambayoyin da maneman labaru suka yi masa sai ya ce, a duniya Sin kasa daya kawai, Koda yake har yanzu ba a samu dinkuwar bangarori biyu ba tukuna, amma ba a canja hakikanin halin Sin kasa daya kawai,Wannan shi ne hakikanin hali na Taiwan na yanzu. Ya kuma bayyana cewa, ba mu so gani dauka dabarar da ba ta lumana ba wajen daidaita matsalar Taiwan, in mai yiyuwa ne za mu yi matukar kokarin ingiza zaman lafiya da dinkuwar kasa daya.Ban da haka kuma ya bayyana cewa, karfafuwar karfin soja na kasar Sin ba zai kawo kurari ga sauran kasashe ba.(Dije)
|