|
|
 |
 |
| Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
| (GMT+08:00)
2005-03-11 16:41:46
|
 |
|
Sashen jiragen sama na babban yankin kasar Sin ya gayyaci masu kula da jiragen sama na yankin Taiwan don tattauna al'amarin tafiye tafiyen jiragen sama tsakanin bangarori biyu kai tsaye
cri
Labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, a ran ll ga watan nan da muke ciki, mataimakin shugaba na kwamitin musaye musaye na zirga zirgar jiragen sama na tsakanin bangarori biyu kuma mamba na zaunannen kwamiti na kungiyar kula da zirga zirgar jiragen sama masu daukar fasinjoji na farar hula na kasar Sin ya rubuta wata wasika zuwa ga shugaban kungiyar cinikin zirga zirga na jiragen sama na birnin Taibei don gayyace shi da ya ba da jagora ga kungiyar masu kula da sha'anin nan don yin shawarwari tare da shi yadda za a yi zirga zirgar jiragen sama masu daukar fasinjoji kai tsaye tsakanin bangarori biyu a ranar bikin gargajiya ta ran 5 ga watan Afrilu na kowace shekara.Kana kuma za a yi shawarwari kan yadda za a yi zirga zirga na jiragen sama masu daukar fasinjoji tsakanin bangarori biyu kai tsaye a sallar bazara ta shekara mai zuwa.(Dije)
|
|
|