Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-09 09:11:10    
Dokar hana ballewa daga kasa tana da amfani ga dinkuwar kasar Sin cikin lumana

cri
A ran 8 ga wata, membobin da ba na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin sun tattauna kan bayanin da Wang Zhaoguo, mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi game da shirin dokar hana ballewa daga kasa a wannan rana, inda suka bayyana cewa, makasudin tsara wannan doka shi ne yaki da kuma hana ayyukan yunkurin 'yancin Taiwan. Wannan doka tana da amfani ga kokarin dinkuwar kasar Sin cikin lumana.

Mataimakin shugaban jam'iyyar Zhi Gong ta kasar Sin kuma memban dindindin na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin Yu Yunbo yana ganin cewa, dokar hana ballewa daga kasa da ake dudduba tana da amfani sosai wajen kokarin daidaita maganar Taiwan ta hanyar lumana da tattabar da zaman lafiya a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. Ban da wadannan kuma, za a fi samun hanyoyin lumana wajen dinkuwar kasar.

Zhang Huajun, memban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin kuma dan jam'iyyar dimokuradiyya mai cin gashin kai ta Taiwan ya ce, shirin dokar hana ballewa daga kasa ya bayyana niyyar kiyaye ikon mulkin kasa da cikakken yankunan kasa ta jama'ar duk kasar Sin. Amma a sa'i daya, da kalmomi da yawa ne wannan shirin doka ya jadadda cewa za a kiyaye halin zaman lafiya a tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan. (Sanusi Chen)