
A ran 8 ga wata, an gabatar da shirin Dokar Hana Ballewa daga Kasa wadda ke jawo hankulan mutane sosai ga zama na 3 na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin ta 10 da ake yi yanzu a nan birnin Beijing. A ran 14 ga wata ne wakilai wadanda suke halartar taron za su jefa kuri'a kan shirin dokar.
Wang Zhaoguo, mataimakin shugaban majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin ya bayyana wa wakilan majalisar muhimman abubuwa na wannan shirin doka da dalilin da ya sa aka tsara wannan shirin doka da ka'idojin har da duk ayyukan da ake bi wajen tsara shirin dokar.
Mr. Wang ya ce, bisa ka'idar da aka tsara a cikin shirin dokar, a tsaya kan ka'idar Sin daya tak tushe ne da ake ciki wajen tabbatar da dinkuwar kasar cikin lumana. Da babbar sahihiyar zuciya ce kasar Sin za ta yi namijin kokari wajen tabbatar da dinkuwar kasar cikin lumana. Amma idan runkunin 'yan neman 'yancin Taiwan sun balle yankin Taiwan daga kasar Sin ta kowane uzuri da ta kowace hanya, ko idan babban al'amarin ballewar Taiwan daga kasar Sin ya faru, ko sharadin neman dinkuwar kasar cikin lumana ya mutu. Dole ne kasar Sin za ta dauki hanyoyi da ba na lumana ba ko sauran wajibabbun matakai domin kiyaye ikon mulkin kasar da cikakken yankunan kasar Sin. (Sanusi Chen)
|