Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-07 17:52:03    
Babban yankin kasar Sin zai cigaba da nuna hali nagari ga 'yanuwa  na Taiwan

cri
A cikin rahoton aikin gwamnatin da ya bayar,Firayim Ministan kasar Sin Wen Jiabao na kasar Sin ya yi bayani kan ayyukan da aka yi kan batun Taiwan har ya samu yabo da wakilan majalisar wakilan jama'ar kasa da 'yan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin da suke halartar tarurrukan da aka saba yi shekara shekara,a sa'i daya sun bayyana cewa kamar yadda ya yi a da babban yankin kasar Sin zai cigaba da nuna halin kirki ga 'yanuwa na Taiwan.

A cikin rahoton aikin gwamnatin,Wen Jiabao ya ce duk abin da ya taimakawa cigaban dangantaka dake tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan da dinkuwr kasa cikin lumana,babban yankin kasar Sin zai yi iyakacin kokarin kammala shi.Mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na kawancen Taiwan Mista Wu Guozhen ya ce alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan batun Taiwan ya shaida kulawar babban yankin kasar Sin kan 'yanuwa na Taiwan.(Ali)