|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-03-06 17:25:50
|
 |
Kafofin yada labarai na Taiwan sun ba da sharha kan jawabin da Shugaban kasa Hu Jintao ya yi
cri
A cikin kundin ketare na jaridar People's daily ta kasar Sin na ran 6 ga wata,an buga wani labari cewa jawabin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi kwanakin baya kan bunkasa dangantaka dake tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan cikin sabon halin da ake ciki ya jawo hankulan mutanen Taiwan sosai.Kafofin yada labarai na Taiwan suna masu ra'ayin cewa jawabin Hu Jintao ya bayyana sabon nufi da halin kirki.
Jaridar Lianhebao ta bayar da wani sharhi cewa a cikin jawabinsa Hu Jintao ya bayyana manufar da ake bi kan batun Taiwan daga dukka fannoni.Hu Jintao ya nuna halin kirki ga sassan da lamarin ya shafa a cikin ra'ayinsa guda hudu dangane da yalwata dangantaka tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan.Muddin ya amince da ka'idar Sin daya,ko shi wane ne kowace jam'iyya,babban yankin kasar Sin ya yi maraba yana so ya yi tattaunawa da su wajen bunkasa dangantaka tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan da neman dinkuwar kasa cikin lumana.(Ali)
|
|
|