Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-03-05 16:39:30    
Wakilan NPC da 'yan CPPCC sun yaba wa jawabin da Hu Jintao ya yi kan maganar Taiwan

cri
A ran 4 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bayar da wani muhimmin jawabi kan yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Pacific a cikin sabon hailn da ake ciki yanzu. Wannan jawabi ya samu amsoshi da yawa daga wajen wakilan dake halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin da membobin da ke halartar taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin a nan birnin Beijing. Sun bayyana cewa, wannan jawabi ya bayar da cikakkiyar sahihiyar zuciya da fatan alheri kan yadda za a tabbatar da karkon dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin takun Taiwan kuma za a iya yin namijin kokari wajen dinkuwar kasar cikin lumana. Wannan jawabi ya kuma bayyana niyyar kiyaye da tabbatar da ikon mulkin kasa da cikakken yankunan kasar. Sabo da haka, sun nuna cewa, wannan jawabi zai yi tasiri sosai a nan gaba. (Sanusi Chen)