Jawabin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi a ran 4 ga wata kan yadda za a raya dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan a cikin sabon halin da ake ciki ya samu amsoshi kwarai daga mutanen Taiwan da na Hongkong kuma da na Macao. Bi da bi ne, suka bayyana cewa, ya kamata hukumar Taiwan ta fahimci sahihiyar zuciya da fatan alheri da matsayi da niyya da wannan jawabi ke bayyana, kuma ta yi wani zabe daidai a tarihi domin tabbatar da dinkuwar mahaifa cikin lumana.
Shugaba Chen Qinming na kawancen Taiwan na dinkuwar kasar ya nuna cewa, jawabin da Hu Jintao ya yi yana daidai da halin da ake ciki yanzu, yana kuma mai da hankali kan moriyar jama'ar Taiwan. Ba ma kawai jawabin ya nuna kyakkyawar makomar da kokarin neman dinkuwar kasar Sin cikin lumana zai kai wa 'yan uwanmu na Taiwan ba, har ma a fili ne ya bayyana bala'in da ayyukan neman 'yancin kan Taiwan zai kawo wa Taiwan.
He Liangliang wanda ke yin sharhi kan al'amuran duniya a gidan rediyo mai hoto na Phoenix na Hongkong, yana ganin cewa, jawabin Hu Jintao yana bayyana ka'idar da ake bi, kuma yana bayyana hali maras alkibla da ake ciki kan maganar Taiwan. (Sanusi Chen)
|