 Daftarin shirin Dokar Hana Ballewa daga Kasa wadda za a duba shi a gun taron shekara-shekara na shekarar nan na majalisar dokokin kasar Sin, wata dokar da ke raya dangantakar da ke gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan, kuma za ta ingiza ayyukan dinka duk kasar Sin cikin lumana. Wannan doka za ta kuma yi adawa kuma hana yunkurin jawo barakar kasar Sin da wasu masu 'yancin kan Taiwan suke yi, kuma za ta kiyaye zaman lafiya da na karko a yankin Asiya na tekun Pacific. Bugu da kari kuma, nauyin da ke wuyan wannan doka shi ne kiyaye ikon mulkin kasa da cikakken yankunan kasar Sin, tana dacewa da ainihin moriyar kabilar duk kasar Sin.
Jiang Enzhu, kakakin zama na 3 na majalisa ta 10 ta dokokin kasar Sin ya fadi haka ne a gun taron manema labaru na farko da aka yi a ran 4 ga wata a nan birnin Beijing. Mr. Jiang ya ce, wannan doka, wato wata muhimmiyar doka ce, tana bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana nuna sahihiyar zuciya domin kokartawa wajen neman dinkuwar duk kasar Sin cikin lumana. (Sanusi Chen)
|