
Ran 2 ga wata, hukumar 'yan sanda ta kasar Iraki ta bayyana cewa, ran 1 ga wata, dakarun da ba a san su wane ne ba sun yi kisan gilla ga alkalin kotun musamman ta kasar Iraki wadda ke kula da batun binciken laifin Saddam Hussien da manyan jami'ansa Malam Barwez Mohammed Mahmoud Al-Merwani da dansa lauya Aryan Barwez Al-Merwani. Wannan ne karo na farko da aka yi wa alkali da lauya kisan gilla a cikin sama da shekara guda da ta wuce tun bayan kafa wannan kotun musmman.
Haka nan kuma an yi musu kisan gilla ne bayan da kotun musamman ta kasar Iraki ta shelanta a ran 28 ga wata cewa, za ta gurfanar da Barzan Ibrahim Al-Hassan Al-Tikriti, kanen tsohon shugaba Saddam da Taha Yassin Ramadan, tsohon mataimakin shugaban kasar da sauran manyan jama'ai uku a gaban kotun.
An kafa wannan kotun musamman ta kasar Iraki ne a watan Disamba na shekarar 2003 bisa taimakon kudin gwamnatin W. Bush da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 75. Bayan da aka kafa wannan kotun musamman ba da dadewa ba, sai bi da bi aka yi kisan gilla ga 'yan takara 5 wadanda mai yiwuwa ne za su zama alkalan kotun nan. Da ganin haka, ya zuwa yanzu dai ba a bayar da sunayen mambobin wannan kotu da wurin zamanta ba. Ko da yake ma'aikatar shari'a ta kasar Amurka ta aika da mashawartan shari'a da yawa zuwa kasar Iraki, kuma sun sa hannu cikin harkokin tattara abubuwan shaidar laifin Saddam, amma duk da haka suna ta shan wahalhalu.
1 2 3
|