A nan kasar Sin, mulkin kasa ya kasu cikin gida biyar, kason kuma su ne gwamnatin tsakiya da hukumomin larduna da hukumomin birane da hukumomin gundumomi da hukumomin garuruwa da na kauyuka. Tsarin majalisar wakilan jama'a babban tsarin siyasa ne ga kasar Sin. Bisa tsarin mulki na Jamhuriyar Jama'ar Sin, duk mulkin Jamhuriyar Jama'ar Sin na cikin hannun jama'a ne. Majalisar wakilan jama'ar kasa da majalisun wakilan jama'a na matakai dabam daban hukumomi ne da jama'a ke aiwatar da harkokin mulkin kasa. Masu zabe su ne ke zaben wakilan majalisun wakilan jama'a na gundumomi da kauyuka kai tsaye, haka nan kuma mambobin sauran majalisun wakilan jama'a na matakai uku majalisun wakilan jama'a na matakin kasa ne su ke zabansu a fakaice.
Majalisar wakilan jama'ar kasa hukumar koli ce da jama'ar kasar Sin ke aiwatar da harkokin mulkin kasa. Taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasa da aka shirya a shekarar 1954 ya alamanta cewa, an kafa tsarin majalisar wakilan jama'a. Bisa shari'a da dokokin zabe, bangarori 35 kamar su larduna da jihohin kananan kabilu masu aiwatar da harkokin kansu da birane da ke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye da yankin musamman na Hong Kong da Macao da rundunar sojojin kwatar 'yancin kasa ta jama'ar Sin da sauransu su kan zabar wakilan majalisar wakilan jama'ar kasa. Yawan wakilai da suka ci zabin zaman 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 10 a shekerar 2003 ya kai 2985.
Majalisar wakilan jama'ar kasa tana da ikon kafa dokokin kasa, da yin gyare-gyare kan tsarin mulkin kasa, da sa ido ga aiwatar da tsarin mulkin kasa, da kafa dokokin yau da kullum da sauran dokoki da yin gyare-gyarensu, da yin zaben jami'an hukumomin kasa, da na kotuna da hukumomin kai kara, da hukumomin aikin soja, haka zalika tana da ikon tube wadannan jama'ai daga mukamansu. Wannan majalisar kuma tana sa ido ga yadda hukumomi ke aiwatar da ayyukansu, da duba manyan al'amuran kasa da yanke shawara a kai duk bisa tsarin mulkin kasa da dokoki. Duk ma'aikatun hukumomi da majalisun wakilan jama'a suka kafa, suna dauke da nauyi da ke bisa wuyansu game da majalisun nan, haka nan kuma suna karkashin lurarsu.
Wa'adin aiki na ko wace majalisar wakilan jama'ar kasa ya kai shekaru biyar. Kuma zaunannen kwamitin majalisar nan ta kan shirya zaman majalisar sau daya a ko wace shekara.
Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa hukumar din din din ce ga majalisar nan. Majalisar kuma ita ke zaben wakilan zaunannen kwamitin nan. A lokacin da ba a yi zamanta ba, hukumar din din din ke aiwatar da ikon koli na kasa. Bisa abubuwa da aka tanada a cikin tsarin mulkin kasa, mambobin zaunannen kwamitin majalsiar wakilan jama'ar kasa ba su iya rike mukaman hukumomin kasa da kotuna da hukumar kai kara. Zaunanen kwamitin yana kunshe da shugba da mataimakan shugabanni da babban sakatare da wakilai.
|