Li Weiyi , kakakin Ofishin harkokin Taiwan na Majalisar gudanarwar kasar Sin ya bayyana a ran 25 ga watan nan a birnin Beijing cewa , Kwamitin dindindin na Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya fara aikin share fagen tsara dokar adawa da wariyar kasar. Wannan yana da amfani ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na gabobi biyu na Zirin Taiwan da na Asiya da Pacific .
A gun taron watsa labaru da aka shirya , Mr. Li ya ce , a cikin dogon lokacin da ya wuce , babban yankin kasar Sin ya yi kokari sosai don sa kaimi kan yalwatuwar huldar dake tsakanin gabobi biyu da dinkuwar kasar Sin cikin lumana . Amma duk da haka Hukumar Taiwan ta karfafa aikace-aikacen wariyar kasar . Kungiyoyin neman ba wa Taiwan mulkin kai sun kawo barazana mai tsanani ga mallakar kai da cikakken yankin kasar Sin . Saboda haka kwamitin dindindin na majalisar ya fara aikin share fagen.
|