Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-25 16:59:58    
Babban yankin kasar Sin zai sa himma wajen shigo da kayayyakin noma zuwa kasuwanninsa

cri
Labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, a ran 25 ga watan nan da muke ciki, a nan birnin Beijing, wani jami'I na sashen da abin ya shafa na babban yankin kasar Sin ya bayyana cewa, za mu yi kokarin habaka shigor da kayayyakin gona na yankin Taiwan zuwa kasuwannin babban yankin kasar Sin, Kana kuma za a nuna himma kan hadin guiwar sha'anin noma.

A gun taron gana da maneman labarun da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majaliar gudanarwa ya shirya a wannan rana, an bayyana cewa, babban yankin kasar Sin yana maraba da mutane na sassan aikin gona da su zo babban yankin kasar Sin don neman kara samu bunkasuwar sha'anin gona,Kana kuma muna son yin shawarwari tare da mutane na sassan gona wajen kara yin hadin guiwar aikin noma na tsakanin bangarori biyu don biyan moriyar 'yan uwa na bangarorinmu biyu.(Dije)