Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-22 18:07:23    
Kasar Sin ta yaba wa kasar Finland saboda ta tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya

cri
A ran 22 ga wannan wata, a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, lokacin da ya yi shawarwari da sakataren gudanarwa na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Finland Mansala da ke yi ziyara a kasar, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Yesui ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin ya yaba wa bangaren kasar Finland saboda ya tsaya tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Mr. Zhang ya darajanta dangantakar sada zumunci da ke tsakanin kasashen nan 2.

Daga nasa wajen kuma, Mr. Mansala ya bayyana cewa, a shekarun nan da suka wuce, manyan jami'an kasashen nan 2 sun rika kai wa juna ziyara, haka kuma, kasashen nan 2 sun kara yin hadin gwiwa a fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki da al'adu da kuma kimiyya da fasaha. Bangaren kasarsa ya gamsar da bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasashen nan 2. Ban da wannan kuma, bangarorin nan 2 sun yi musayar ra'ayoyinsu kan manyan al'amuran duniya da na shiyya-shiyya na yanzu.(Tasallah)