Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-22 16:10:42    
Gwamnatin kasar Togo tana shan wahala

cri

Kwanan baya ba da dadewa ba,kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammancin Afirka ta sanar da cewa,za ta yi takunkumi ga gwamnatin kasar Togo daga dukkan fannoni ta yadda za a tilasta wa shugaban kasar Faure Gnassingbe da ya yi murabus daga mukaminsa.A sa`i daya kuma,mutane dake cikin kasar Togo bi da bi ne suka yi ta yin zanga-zanga bisa babban mataki don matsa lamba ga gwamnatinsu.A halin da ake ciki yanzu,gwamnatin kasar Togo tana shan wahala tana cikin mawuyacin hali.

A ran 19 ga wata,kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammancin Afirka ta bayar da wani rahoto,inda ta bayyana cewa,kwanakin baya shugaban kasar Togo Faure ya sanar da cewa zai yi babban zabe a kasar,wannan bai dace da rokon da kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammancin Afirka ta yi wa kasar ba game da maido da tsarin mulkin kasa a kasar daga dukkan fannoni,shi ya sa kungiyar ta tsai da cewa za ta yi takunkumi ga kasar Togo daga dukkan fannoni,abubuwan takunkumin sun hada da: za a soke matsayin mamba na kasar Togo a cikin kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammancin Afirka cikin gajeren lokaci da janye jakadun kasashen wakilan kungiyar dake wakilci a kasar Togo da hana jigilar makamai ga kasar Togo da kuma yi wa shugabannin gwamnatin kasar da sauran jami`an kasar takunkumi wajen yawon shakatawa a shiyya-shiyya da sauransu.

A ran 5 ga wata ne,shugaban kasar Togo Gnassingbe Eyadema ya riga mu gidan gaksiya saboda ciwon zuciya,daga baya,rundunar sojoji masu damara na kasar ta sanar da cewa, don tabbatar da tsaron lafiyar kasar,za ta mika wa dansa Faure ikon shugaban kasar.Bayan wannan,majalisar dokokin jama`a ta kasar Togo ta tube tsohon shugaban majalisar Fambare Ouattara Natchaba daga mukaminsa,kuma ta zabi Mr.Faure da ya zama sabon shugaban majalisar dokokin jama`ar kasar Togo,kuma ya fara rike mulkin kasar.Ban da wannan kuma,majalisar dokokin kasar Togo ta gyara tanadin da abin ya shafa dake cikin tsarin mulkin kasar game da cewa dole ne a yi babban zaben shugaban kasa a cikin kwanaki 60 bayan mutuwar tsohon shugaban kasar,ta yarda da Mr.Faure da ya zama shugaban kasar kafin a yi babban zaben shugaban kasa a shekara ta 2008.A ran 7 ga wata,Mr.Faura ya yi rantsuwar kama mulkin kasar Togo wato ya zama sabon shugaban kasar.

Bayan wannan,bi da bi ne al`ummar kasashen duniya musamman ma kasashen Afirka suka bayar da sanar`a,inda suka soki kasar Togo saboda ta gyara tsarin mulkin kasa,aikin da ake yi a kasar Togo shi ne `boren siyasa` da hukumar soja ta kasar Togo ta yi.Kawancen kasashen Afirka da kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammancin Afirka da wasu kasashen Afirka bi da bi ne suka roki gwamnatin kasar Togo da ta maido da tsarin mulkin kasa na da nan da nan ba tare da bata lokaci ba,kuma ta shirya babban zabe cikin lokaci,in ba haka ba,za a yi mata takunkumi.

Saboda haka,Mr.Faure ya yi rangwame,a ran 18 ga wata,ya sanar da cewa za a yi babban zaben kasar a cikin kwanaki 60.Amma a sa`i daya kuma,ya bayyana cewa,kafin babban zaben da za a yi,zai ci gaba da zama shugaban kasar Togo.Wannan ya sa kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammancin Afirka ta tsai da cewa za ta yi wa kasar Togo takunkumi nan da nan.Daga baya,zaman al`ummar kasashen duniya wadanda ke ciki suka hada da kawancen kasashen Afirka da kawancen kasashen Turai da kasar Amurka da kasar Fasanra da sauransu sun nuna goyon bayansu ga wannan.Duk wadannan sun sa gwamnatin kasar Togo ta shiga mawuyacin hali.

Ra`ayin bainal jama`a yana ganin cewa,ra`ayin kawancen kasashen Afirka yana da babban amfani ga makomar kasar Togo.Idan kawancen kasashen Afirka ya yi wa kasar Togo takunkumi,to,kasar za ta kasance cikin zaman kadaici.

Game da wannan,me gwamnatin kasar Togo za ta yi?Wannan shi ne abin da za a sa ido a gani.(Jamila Zhou)