A ran 21 ga wata,jaridar `People`s Daily` wato jaridar hukumar kasar Sin ta buga wani bayani,inda ta nuna kiyayya ga kasar Amurka da kasar Japan saboda taron kwamitin yin tattaunawa kan tsaron lafiyar kasashen nan biyu ya bayar da wata sanarwa kan matsalar Taiwan.
Bayanin ya ce,sinawa suna fatan halin da zirin Taiwan ke ciki zai zauna da gindinsa.
Idan kasar Amurka da kasar Japan suna so su kiyaye zaman lafiya da zaman karko a shiyyar Asiya da Pasific,to,kamata ya yi su cika alkawarin da suka yi game da nacewa ga ka`idar kasar Sin daya tak a duniya.(Jamila Zhou)
|