Ya zuwa ran 20 ga wata,an kammala aikin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan na kasar Sin a bikin bazara na gargajiyar kasar Sin cikin nasara.Kwararrun mutanen da abin ya shafa sun yi nuni da cewa,kodayake wannan aiki ya taimaka wajen sassauta huldar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan,amma ba zirga-zirga ce ta kai tsaye tsakanin gabobin biyu ba,shi ya sa ana iya cewa,ba zai kawar da hulda mai tsanani dake tsakanin gabobin biyu ba.
Game da wannan,shehun malami Zhang Guanhua wanda ya zo daga ofishin yin nazari kan matsalar Taiwan na cibiyar yin nazari kan kimiyyar zaman al`umma ta kasar Sin ya ce,dalilin da ya sa aka yi wannan aiki shi ne don biyan bukatun jama`ar kasa musmaman ma don biyan bukatun `yan uwa na Taiwan,wannan aiki aikin kasuwanci ne kawai.Shehu malami Zhang Guanhua ya ci gaba da cewa,muddin dai hukumar Taiwan ta yi na`am da ka`idar kasar Sin daya tak a duniya,za a iya kyautata huldar dake tsakanin gabobin biyu.(Jamila Zhou)
|