A gun taron manema labarun da aka saba yi a ran 17 ga wata a nan birnin Beijing, Kong Quan, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan sassan da abin ya shafa na Amurka za su nazarci halin da ake ciki a mashigin teku na Taiwan sosai, kuma su cika alkawarin da gwamnatoci daban-daban na tarihin Amurka suka dauka na aiwatar da manufar kasar Sin daya kawai a duniya, da yin adawa da masu neman samun "mulkin kan Taiwan"
Kong Quan ya ce, kada Amurka ta ba da alamar kuskure ga mutane masu jawo baraka na neman samun mulkin kan Taiwan, su yi ayyuka masu amfani ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, haka ma ga kiyaye zaman lafiya da zama mai dorewa na mashigin tekun taiwan.
Kong Quan ya bayyana cewa, domin hana yunkurin da masu jawo baraka suke yi na neman mulkin kan Taiwan, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta fara aikin kafa dokar yin adawa da masu jawo baraka ga kasar, wannan zai taimaka ga samun zaman lafiya a shiyyar. (Umaru)
|