Kwanan baya,a hukunce shugaban kasar Amurka Bush ya gabatar da wani shirin kara kasafin kudi wanda yawansa ya kai kudin dallar Amurka biliyan 81 da miliyan 900 ga majalisar dokokin kasar,nufin wannan shiri shi ne don samar da kudi ga aikin soja da kasar Amurka za ta yi a kasar Iraki da kasar Afghanistan a wannan shekara.Mutane dake adawa da yaki da `yan jam`iyyar dimokuradiya na kasar Amurka suna ganin cewa,manufar kuskure da gwamnatin Bush take aiwatarwa ta sa kasar Amurka tana shan wahalar yakin Iraki da yakin Afghanistan ke kawo mata,kuma kasar Amurka za ta ci gaba da ware kudi da yawan gaske kan wannan.
Tun bayan aukuwar al`amari a ran 11 ga watan Satumba na shekarar 2001,kasar Amurka ta riga ta ware kudi da yawan gaske kan yakin Afghanistan da yakin Iraki,gaba daya yawansa ya riga ya zarce dallar Amurka biliyan 200,yawan kudin da aka ware kan sake gina kasar Iraki da kasar Afghanistan ya riga ya kai dallar Amurka biliyan 27.A lokacin zafi na shekarar bara,fadar shugaban kasar Amurka wato `the white house` ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta ba ta kudi dallar Amurka biliyan 25 domin aikin soja da aikin sake gina kasa da sojojin kasar Amurka za su yi a shekara ta 2005.A ran 14 ga wata,shugaban kasar Bush ya sake rokon majalisar dokokin kasar da ta kara ba da kudin aiki da yawansa ya kai dallar Amurka biliyan 81 da miliyan 900.Daga nan,gaba daya yawan kudin da kasar Amurka ta ware kan yakin Iraki da yakin Afghanistan da aikin sake gina kasashen nan biyu ya riga ya wuce dallar Amurka biliyan 300.
Game da wannan,`yan majalisar dokoki da suka zo daga jam`iyyar dimokuradiya da mutane wadanda suke adawa da manufar yakin Iraki na kasar Amurka ba su yarda da wannan ba.Wasu suna ganin cewa,a kowane mako,yawan kudin da kasar Amurka ta ware ya kai fiye da dallar Amurka biliyan daya,amma kawo yanzu,ba a sassauta hargitsin nuna karfin tuwo dake faruwa a cikin yankin kasar Iraki ba,kuma ba a sami ci gaba a fannin sake gina kasar Iraki ba.Ana iya cewa,duk wadannan kudade ba su iya kubutar da sojojin kasar Amurka daga mawuyacin hali ba.`Dan majalisar dattijai da ya zo daga jam`iyyar dimokuradiya Robert Byrd ya bayyana cewa,kodayake wadannan kudade za su taimakawa sojojin kasar Amurka dake zaune a kasar Iraki,amma ba zai amfanawa halin da kasar Iraki ke ciki ba.Wasu mutane kuma suna cikin zulumi saboda gibin kudin kasar Amurka yana kara karuwa a kwana a tashi.An kimmnata cewa,a wannan shekara,yawan gibin kudin kasar zai kai kudin dallar Amurka biliyan 427.
Masu lura da al`amuran yau da kullum suna ganin cewa,kodayake shirin nan ya gamu da kiyayya daga bangarorin da abin ya shafa,amma da sauki zai sami yarda daga majalisar dokokin kasar wadda ke karkashin sarrafawar jam`iyyar Republic.A ran 14 ga wata,shugaba Bush na kasar Amurka ya bayar da wata sanarwa,inda ya bayyana cewa,za a yi amfani da yawancin kudaden a kan aikin taimakawa sojojin kasar Amurka dake zaune a kasar Iraki,ban da wannan kuma,za a yi amfani da su a kan aikin kama `yan ta`adda.Kwamitin ba da kudi zai jefa kuri`a kan wannan shiri a farkon watan Maris mai zuwa,daga baya,cikakken taron majalisar wakilai zai kada kuri`a kan wannan.
Masu lura da al`amuran yau da kullum suna ganin cewa,yawan kudin da kasar Amurka ta ware kan aikin sake gina kasar Iraki da kasar Afghanistan ya riga ya zarce kimmantawar gwamnatin Bush.(Jamila Zhou)
|