Ranar sallar bazara, wato sallar gargajiya ta kabilun kasar Sin ta kusanyo, tun daga ran 5 ga wata, 'yan kasuwar Taiwan sun yi shatar jiragen sama a yanayin sallar bazara, an shiga lokaci na biyu na jigilar fasinja.
Tun daga ran 5 zuwa ran 9 ga watan nan, da akwai jiragan sama guda 34 da ke shawagi daga babban yankin kasar Sin zuwa Taiwan, jiragan saman nan suna hade da Beijing da Shanghai da Gwanzhou da Taibei da Gaoxiong. Wasu 'yan kasuwa da iyalansu da ke gudanar da harkokinsu a babban yankin kasar Sin , za su shiga jiragen sama don komawa Taiwan, yayin da'yan uwa na Taiwan zasu zo nan babban yankin kasar Sin cikin jiragen saman nan don haduwa da iyalansu.(ASB)
|