
A ran 3 ga wata, Sun Yafu, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar kulla hulda tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan da Li Yafei, babban sakataren kungiyar sun kai wa Wang Daohan, shugaban kungiyar ziyarar girmamawa a birnin Shanghai bayan da suka je Taiwan domin mika ta'aziyyar rasuwar Gu Zhenfu, shugaban "Asusun yin mu'amala tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan" a madadin Wang Daohan.
Bayan da Wang Daohan ya gana da su, Sun Yafu ya gaya wa manema labaru cewa, ziyarar da suka yi a Taiwan a madadin Wang Daohan ba ma kawai ta nuna girmamawa da begen da aka yi wa Gu Zhenfu ba, har ma ta nuna wa jama'ar Taiwan girmamawa. Mr. Sun ya yi hasashen cewa, a nan gaba za a cigaba da yin musaye-musaye da mu'amala da shawarwari a tsakanin hadaddiyar kungiyar kulla hulda tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan da asusun yin mu'amala tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan. (Sanusi Chen)
|