Mataimakin shugaban kungiyar kula da dangantaka tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan Sun Yafu da kuma babban sakatare na kungiyar Li Yafei sun isa birnin Taibei a ran 1 ga watan nan da yamma domin nuna ta'aziyya ga Gu Zhenfu a madadin wakilan shugaban kungiyar Wang Daohan bisa gayyatar da iyalan Gu Zhenfu suka yi musu.
Shugaban hukumar gudanarwa ta asusun yin mu'amala tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan Gu Zhenfu ya rasu a ran 3 ga watan Janairu a birnin Taibei, kuma shekarunsa ya kai 88.
Bisa labarin da muka samu, an ce, a ran 2 ga watan nan Sun Yafu da Li Yafei za su dawo.(Kande Gao)
|