Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-31 10:03:58    
Wakilan shugaban hadaddiyar kungiyar kulla hulda tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan za su je Taiwan don nuna ta'aziyya ga rasuwar Gu Zhenfu

cri
Bisa gayyatar da iyalan Gu Zhenfu, wato babban daraktan "asusun yin mu'amala tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan" wanda ya riga mu gidan gaskiya suka yi, a madadin shugaba Wang Daohan na hadaddiyar kungiyar kulla hulda tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan ne, mataimakin shugaba Sun Yafu da kuma babban sakatare Li Yafei na kungiyar za su tashi zuwa birnin Taibei don mika ta'aziyya ga rasuwar Gu Zhenfu.

A ran 30 ga wata, kakakin ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, wannan tafiyar da Sun Yafu da Li Yafei za su yi ba za ta shafi mu'amalar da ke tsakanin hadaddiyar kungiyar kulla hulda tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan da kuma asusun yin mu'amala tsakaninsu da dai sauran maganganu da suke da nasaba da dangantakar da ke tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan ba. An ce, a gobe ran 1 ga watan Faburairu, za su tashi ne daga birnin Shanghai, kuma kashegari za su komo.(Lubabatu Lei)