Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 28 ga watan nan a birnin Beijing , Jia Qinglin , shugaban Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya bayyana cewa , a karkashin ka'idar kasar Sin daya kawai, batutuwan yin shawarwari a tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan a bude su ke , kuma fannonin shawarwarin masu yawa ne .
Mr. Jia ya kuma ce , muddin hukumar Taiwan daga yanzu ta fara amincewa da ka'idar Kasar Sin daya tak a bayyane , to , nan da nan za a farfado da tattaunawa da shawarwari a tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan , kuma kowace matsala za mu tattauna a kanta ciki har da sa aya kan halin gaba da gaba da kafa amincewar soja da matsayin Taiwan a duniya da kuma matsayin siyasa da hukumar Taiwan ke ciki .(Ado)
|