|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-01-26 18:05:02
|
Mu'amalar tsakanin jama'ar gabobi biyu na Zirin Taiwan a shekarar bara ta sami sabon ci gaba
cri
Wakilin Rediyon Kasar Sin ya sami labari cewa , A ran 26 ga watan nan a birnin Beijing , Li Weiyi , kakakin Ofishin kula da harkokin Taiwan na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa , a shekarar 2004 , ma'amalar tsakanin jama'ar gabobi biyu na Zirin Taiwan a fannoni daban daban ta sami sabon ci gaba.
Mr. Li ya yi wannan bayyani ne a gun taron manema labarun da aka saba yi a wannan rana. Ya ce , a wannan shekara , babban yankin kasar Sin zai ci gaba da sa kaimi kan mu'amalar jama'ar gabobi biyu da musaye-musayen dake fannin tattalin arziki da al'adu tare da babban sahihanci da iyakacin kokari kuma kamar yadda ya yi a da . Kuma babban yankin zai samar da wata damar farfado da tattaunawa da shawarwari cikin hanzari bisa ka'idar kasar Sin daya tak.(ADO)
|
|
|