A gun nunin "zanen-zane masu samun lambobin yabo" na duk kasar Sin da aka yi kwanan baya ba da dadewa ba, wani zanen fenti mai suna "Da karfe 9 a ran 9 ga watan Satumba na shekarar 1945 a birnin Nanjing" wanda ya samu lambar zinariya ya jawo hankulan mutane sosai, wanda kuma ya samu yabo daga wajen kwararru da 'yan kallo duk gaba daya. Jama'a masu sauraro, yanzu bari mu yi muku wani bayani kan wannan zane da mai yin zanen wato Chen Jian.
Zanen fenti mai suna "Da karfe 9 a ran 9 ga watan Satumba na shekarar 1945 a birnin Nanjing" ya bayyana yadda gwamnatin Jamhuriyar kasar Sin ta amince da sarandar da Japan ta yi mata a shekarar 1945. Fadin zanen ya kai kusan mita 6, tsayinsa kuma ya kai kusan mita 2, an yi zanen cikin nitsuwa, mutane da yawa na tarihi sun yi kamar suna da rai. Zanen ya takaita tarihin yakin dagiya kan harin Japan da jama'ar kasar Sin suka shefe shekaru 8 suna yin sa cikin jaruntaka. A gun nunin wakilinmu ya ga 'yan kallo da yawa suna tsaye suna kallon wannan zane cikin shiru.
Wanda ya yi zanen Chen Jian ya bayyana cewa, makasudinsa na yin wannan zane shi ne domin sake bayyana wa mutane wani lokacin tarihin da ba za a iya mantuwa da shi ba. Ya ce?"Tarihi ya riga ya wuce, yanzu muna waiwayen tarihi ne, ya kamata mu bayyana wa mutane hakikanin halin da ake ciki a wancan lokaci. Muhimmin dalilin da ya sa wannan zane ya jawo hankulan mutane shi ne sabo da ya nuna himmantacen halin al'ummar kasar Sin."
Mai zane Chen Jian yana da shekaru 54 da haihuwa, wanda aka haife shi a lardin Jiangsu da ke kudu maso gabashin kasar Sin, yana aiki a birnin Nanjing, hedkwatar wannan lardi, kuma ya dukufa kan ayyukan zane-zane kan batun yaki, dakin zanensa yana kusa da tsohon mazaunin wurin bikin amincewa da saranda da aka yi a wancan zamani a shiyyar yakin kasar Sin ta babban yakin duniya na 2, shi ya sa Chen Jian ya yi nufin yin wannan zane.
Chen Jian ya fara yin wannan zane daga shekarar 1993, bayan da ya shafe shekaru 5 yana yin shirin zane na farko, sai ya sake yin shirin zane na 2 har ya gama zanen kwata-kwata, wato bai gama yin zane ba sai cikin shekaru 10 da suka wuce. Ya bayyana cewa, "Manufar da na tsayar a farkon-farko wajen yin wannan zane ita ce, bayan da na yi wannan zane, idan wani yana son ya yi zane daban kan wannan batu, sai ya iya daukar wannan zane tawa bisa matsayin abin dogaro."
A cikin zane mai suna "Da karfe 9 a ran 9 ga watan Satumba na shekarar 1945 a birnin Nanjing" da Chen Jian ya zana, da akwai mutane fiye da 100. Kafin ya zana wadannan mutane, da farko ya yi binciken hotunan da abin ya shafa, kuma ya yi mutum-mutuminsu, daga baya kuma sai ya fara yin zanen, sabo da haka mutanen da ya zana dukkansu suna nuna rayayyen hali.
Bayan da aka nuna wannan zane da Chen Jian ya zana cikin shekaru 10, nan da nan ya jawo hankulan mutane sosai, kwararru da 'yan kallo sun nuna masa matukar yabo, kuma wannan zane ya ci zaben samun lambar zinariya na nunin zane-zane na 10 na duk kasar Sin. Feng Yuan, shugaban dakin nuna zane-zanen kasar Sin ya bayyana cewa, "Muna iya gane cewa, mai yin zanen ya yi matukar kokari kuma ya yi gyare-gyare da yawa lokacin da yake yin wannan zane, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce ba safei akan ga irin wannan zane da suke bayyana muhimman batutuwan tarihi ba." (Umaru)
|