Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Kong Quan ya ce, a bayyane ne bangaren kasar Amurka ya riga ya tabbatar wa bangaren kasar Sin cewa, bai gayyaci kuma ba zai amince da kungiyar wakilan hukumar Taiwan zuwa gun bikin yin rantsar karb da shugaba Bush ba.
Mr. Kong ya fadi haka ne a gun taron manema labaru da aka yi a yau a nan birnin Beijing lokacin da wani wakili ya tambaye shi mene ne sharhinsa game da labarin da wasu kafofin Taiwan suka bayar, cewar hukumar Taiwan za ta aika da wata kungiyar manzon musamman wadda ke karkashin Li Yuanzhe zuwa bikin rantsar da shugaba Bush. Wannan kungiya ta hada da wasu manyan jami'an hukumar Taiwan.
Kong Quan ya ce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta mai da hankali kan wannan labari, kuma ta gabatar da ra'ayinta ga bangaren kasar Amurka. A bayyane, bangaren kasar Amurka tabbatar da cewa, bai gayyaci kuma ba zai amince da kungiyar manzon musamman ta Taiwan ba. (Sanusi Chen)
|