|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-01-18 09:14:30
|
 |
Batun Taiwan ya shafi dangantaka tsakanin Sin da Amurka
cri
A ran 17 ga wata a nan birnin Beijing,yayin da wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mista Tang Jiaxuan ya gana da wata tawagar kwamitin kasa mai kula da manufofin harkokin waje na Amurka wadda take ziyara a kasar Sin,ya bayyana cewa matsalar Taiwan muhimmiyar matsala ce da ta shafi dangantaka tsakanin kasar Sin da Amurka a dukkan fannoni,daidaita matsalar nan yadda ya kamata muhimmin abu ne na tabbatar da cigaban dangantaka dake tsakanin kasashen nan biyu.
Ya bayyana cewa ayyuakan jawo baraka da mahukuntan Taiwan na Chen Shuibina suke yi shi ne sanadin hali mai tsananni da ake samu a dangantaka ta tsakanin gabbobi biyu,kuma ainihin barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan da bangaren Asiya da tekun Pacific.Gwamnatin kasar Sin ta nace ga bin muhimmiyar ka'ida wato "neman dinkuwr kasa cikin lumana da kasa daya da tsarin mulki biyu",ko yaushe da sahihiyar zuciya ta yi iyakacin kokarinta na neman dinkuwar kasa cikin lumana.duk da haka ko kusa ba ta yarda a balle Taiwan daga yankunan kasar Sin ko ta suna da hanya yaya.Ya ce kasar Sin ta yi fatan Amurka da ta yi kome tare da la'akari da moriyar duniya gaba daya da kare zaman lafiya da kwanciyar hanka na zirin Taiwan da moriyar tarayya ta kasar Sin da Amurka.(Ali)
|
|
|