|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-01-10 17:53:17
|
Mai yiwuwa ne, jiragen saman fasinja da aka yi shatansu za su yi zirga-zirga a tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan na kasar Sin
cri
Ran 10 ga wata, Malam Gao Hongfeng, mataimakin shugaban babbar hukumar kula da zirga-zirgar fasinja ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, idan babban yankin kasar Sin da sassan da abin ya shafa na Taiwan na kasar sun yi kokari cikin sahihanci, to, mai yiwuwa ne, jiragen saman fasinja da aka yi shata za su yi zirga-zirga tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan a lokacin babbar sallar gargajiya ta al'ummar kasar Sin wato "Spring Festival ".
Malam Gao ya yi wannan kalami ne yayin da yake ganawa da kungiyar masu neman yin zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta Taiwan wadda ke karkashin jagorancin Malam Zeng Yinquan, shugaban zartaswa na kwamitin kula da manufofi na tsakiya na Jam'iyyar Guomintang. (Halilu)
|
|
|