A gun taron ganawa da manema labarun da aka shirya a ran 21 ga watan nan a nan birnin Beijing, Liu Jianchao, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya ce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta fara aikin kafa dokar yin adawa da aikin jawo wa kasa baraka ne don hana aikace aikacen wai 'yancin kan Taiwan, aikin nan zai yi amfani a wajen kiyaye zaman lafiya da zama mai dorea da wadatar Taiwan da shiyyar Asia da tekun Pacific.
A ran 17 ga watan nan ne taron shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasa ya tsai da kudurin fara aikin kafa dokar yin adawa da aikin jawo wa kasa baraka. Liu Jianchao ya ce, gwamnatin kasar Sin ta tsaya kan ka'idar dinke kasa cikin lumana, kasa daya amma tsarin mulki biyu, amma ko kusa ba ta yarda da a balle Taiwan daga kasar Sin ba. (Dogonyaro)
|