Ran 6 ga wata a birnin Amman, babban birnin kasar Jordan an yi kwana daya ana wani taron ministocin harkokin waje na kasashen da ke makwabtaka da kasar Iraq . Mahalartan taron sun nuna babban goyon baya ga babban zaben Iraq da za a yi a ran 30 ga watan nan, kuma sun tabbatar da cewa, ba za su shiga harkokin gida na Iraq ba, sun kirayi jama'ar Iraq da su shiga zaben da ke da kudurin makomarsu. Masu binciken al'amura sun nuna a ganinsu cewa, kiran taron nan da alkawarin da aka dauka, sun shimfida wani muhalli mai kyau domin babban zaben da za a yi a Iraq.
Kasashe mahalartan taron sun hada da kasashen da ke kewayen Iraq, wato ministocin harkokin waje na kasashe 5 kamar Jordan da Kuwait da Syria da Sauddiya da Turkey, da mataimakin ministan harkokin waje na Iran da ministocin harkokin waja na kasashe 3 wato Iraq da Masar da Bahrain, da Ashraf Qazi wakilin musanman na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyakan batun Iraq. Wani babban batu na taron shi ne yin hasashe kan halin da ake ciki gabannin babban zaben Iraq da daidaita matsayin babban zaben Iraq.
Bayan an yi shawarwari har cikin tsawon sa'o'I sama da 4, a karshe dai gaba daya ne taron ya zartas da wata sanarwa, wacce a ciki aka sake karfafa girmama mallakar kai da yancin kai da cikakken yankin kasa da dinkuwar kasa na Iraq da ka'idojin rashin yin shisshigi cikin harkokin gida da na abota ta makwabtaka. Sanarwar ta amince cewa jama'ar Iraq sun more ikonsu na neman kwanciyar hankali da zama mai dorewa da yancin tsaida makomarsu ta hanyar demokuradiyya, sanarwar ta kuma yi alkawarin cewa za ta taimakawa jama'ar Iraq wajen cim ma burinnan. Sanarwar ta karfafa cewa, bisa kuduran da al'amarin nan ya shafa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta ba da taimakonta da shugabanci cikin sake raya kasar Iraq. Sanarwar ta karada cewa, bayan rundunar sojoji ta kasashe da yawa da ke jibge cikin Iraq sun tabbatar da zaman dorewar siyasa cikin kasar, nan da nan su janye jikinsu da Iraq , kuma kamata ya yi bangaren Iraq ya yi hakuri sosai, don a magance daukan makamai da nuna karfi ga jama'a farar hula. Sanarwar tana fata bangarorin da al'amarin nan ya shafa za su dauki dabaru masu amfani don taimakawa Iraq wajen tabbatar da zama mai dorewa, musamman kara sa ido da harkokin kula da shiyyar iyakar kasa da ke hade da yankin Iraq, da hana shigar da 'yan ta'adda cikin Iraq, da katse samar musu da makamai da kudade. Ashraf Qazi babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma wakilin musanman na batun Iraq, kafin taron ya gaya wa manema labaru cewa, a taimakawa Iraq don ta ci nasara kan babban zabe, zai dace da babbar moriyar kasashen da ke makwabtaka da ita, ciki har da kasar Iran. Kafin taron ministan harkokin waje Hoshyar Zebari na Iraq ya nuna cewa, labarin da kasarsa za ta yada a gun taron shi ne, kasashen da ke makwabtaka da Iraq, ciki har da kasar Iran su yi hakuri, kada su yi shishigi ga babban zabe, su yi tasiri ga sakamakon babban zaben.
Masu binciken al'amuran yau da kullum sun nuna a ganinsu cewa, taron ya nuna cikakken goyon baya ga Iraq da ta yi babban zabe cikin daidai lokaci kuma ana fata galiban jama'ar Iraq za su shiga babban zabe, za su ba da tasiri mai muhimminci sosai ga gardamar da aka yi kan ko za a yi babban zaben Iraq cikin daidai lokaci. (ASB)
|