Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar a ran 31 ga wata,an ce sabon binciken da kafofin yada labarai na Taiwan suka yi domin jin ra'ayoyin jama'a ya yi nuni da cewa kashi sama da 80 cikin dari na mutanen Taiwan suna kuka da mahukuntan dake tsibirin Taiwan kuma a ganinsu babu adalci a zamantakewar al'umma wadanda suka fi yawa a cikin shekaru goma da suka wuce.
Binciken nan da jaridar Lianhe ta Taiwan ta yi a wannan shekara ya kuma yi nuni da cewa kashi sittin cikin kashi dari na mutanen dake cikin tsibirin Taiwan sun nuna bacin rai ga makomarsu.
Ban da wannan,wani sakamakon binciken da wata jami'ar Taiwan ta yi ya yi nuni da cewa mutanen da suka yi kuka da mahukuntan Taiwan sun dau kashi 53 cikin kashi dari na dukkan mutanen dake cikin tsibirin Taiwan wanda ya kai matsayin koli cikin shekaru hudu na baya.(Ali)
|