Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-12-29 10:29:54    
Babban zabe na kasar Iraq yana gaban kalubale mai tsanani

cri

Bisa kididigar da aka yi ba ciakakke ba an ce, daga ran 26 zuwa ran 28 ga watan nan, a cikin farmakokin da aka kai wa sojojin Amurka da ke a Iraq da sojojin tsaron kasar Iraq da 'yan sanda, a kalla mutane 74 sun rasa rayukansu, mutane daruruka sun samu rauni. A ran 28 ga watan nan kawai mutane 42 sun rasa rayukansu, yawancinsu 'yan sanda da sojojin tsaron kasa ne, a Dijla da ke kusa da Tikrit wato garin tsohon shugaba Sadam a arewacin kasar Iraq, dakaru sun harbe 'yan sanda 12, kuma sun mamaye ofishin 'yan sanda, sa'an nan kuma sun rushe wannan ofis. A ofishin 'yan sanda na garin Ishaki da ke kudu da Samarra, sansanin yin adawa da sojojin Amurka, dakaru sun harbe 'yan sanda 4 da wani sojan tsaron kasa. A birnin Bagadaza an kai farmaki ga janar Abud na sojojin tsaron kasar Iraq a kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki, ko da ya ke Abud bai yi kome ba, amma 'yan rakiyarsa sun samu rauni.

A ran 27 ga watan nan da safe an fasa bom a ofishin Abdul Azizal Hakim, shugaban kwamaitin koli na juyin juya hali na Islam, ko da ya ke shi Hakim bai samu rauni ba, ammamutane 13, ciki har da masu gadi sun rasa rayukansu, misali mutane 50 sun samu rauni. Kakakin Hakim ya yi zargi cewa, mabiyan tsohon mulki ne ya shirya wannan farmaki don neman hana shimfida demokradiya a kasar Iraq. 'yan rukunin Shiite sun kai kashi 60 cikin kashi 100 na jimlar yawan mutanen kasar Iraq, sabo da haka kullum rukunin Shiite yana nuna goyon baya ga babban zaben da za a yi. Sabo da haka shugaban rukunin Shiite ya zama mutumin da za a kashe shi.

Banban da rukunin Shiite, rukunin Sunni wanda yawan mutanensu ya kai kashi 1 cikin kashi 5 kawai yana son jinkirtar da babban zaben da za a yi, wato sai a yi babban zabe bayan da sojojin kasashen waje su janye jikinsu daga kasar Iraq. A ganin wadannan jam'iyyun siyasa, a lokacin da sojoji da yawa na Amurka ke hake a Iraq ba za a yi zabe bisa adalci ba. 'yan rukunin Sunni sun kama manyan mukamai a tsohuwar gwamnati, sabo da haka bayan da aka ka da tsohon mulki rukunin Sunni ya fi nuna adawa ga Amurka.

A ran 27 ga watan nan kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun labarta cewa, ma'aikatan MDD da ke ba da taimako ga babban zabe na Iraq sun nuna damuwarsu cewa, yawan masu zaben da za su yi rajasta ba zai kai yadda aka zata ba, mai yiwuwa ne za a kai farmaki ga cibiyar jefa kuri'a, siton ajiye ruku'u na wasu larduna ba su da ayyukan hana farmaki.

An bayyana cewa, har wa yau matsalar zaman lafiya ita ce babban mahani ga babban zaben da za a yi a daidai lokaci. Mutane da yawa suna damuwa cewa, idan ba a iya tabbatar da lafiyar cibiyar jefa ruku'a, to, mutane da yawa ba za su jefa kuri'a ba domin suna jin tsoron farmakin da za a kai musu, sabo da haka za a yi tasiri ga sakamakon zaben da za a yi. A takaice, har yanzu babban zabe na kasar Iraq yana gaban kalubale mai tsanani. (Dogonyaro)