Sansanin sojojin kasar Amurka dake zaune a birnin Mosul na kasar Iraki ya gamu da harin fashewar bom na kunar bakin wake da aka kai musu,wannan ya sa mutanen kasar Amurka su ji ban mamaki.Mai kai hari ya shiga dakin cin abinci na sansanin sojoji kuma ya fasa bom a wurin da sojojin kasar Amurka ke cunkushe,a sanadiyar haka,mutane 22 wadanda ke kumshe da sojojin kasar Amurka 18 da fara hula 4 sun mutu,kasar Amurka ta ji ban mamaki kan wannan.
Sakamakon dumi dumi da aka samu bayan aka yi bincike kan ra`ayin jama`ar kasa ya nuna mana cewa,kashi 56 cikin dari na `yan kasar Amurka ba su goyi bayan yakin Iraki ba.Wannan al`amarin da ya auku a jajibirin bikin kirismeti ya kara sa hankalin mutanen kasar Amurka ya tashi.Mr.Laura Costas,`dan kasar Amurka dake yin zaman rayuwa a jihar Maryland ya aike da wata wasika zuwa ga jaridar `The New York Times`,inda ya zarge gwamnatin kasar Amurka cewa tana aiwatar da manufar harkokin waje mai shan wahala kuma tana gudanar da manufar aikin soja ta kuskure.Ya kirayi mutanen kasar Amurka wadanda ke nuna kiyayya ga yaki su nuna rokonsu wato su bukaci gwamnatinsu da ta janye jiki daga kasar Iraki.Wasu mutanen kasar Amurka kuwa su zargi gwamnatin kasar saboda ba ta dauki jawababbun makamai wajen tsaron lafiyar sojojinta ba,kuma sun tambaye manyan jami`an kasar Amurka cewar me ya sa ba su tura `ya `yansu zuwa kasar Iraki domin yin yaki ba.
Bayan wannan,abu mafi muhimmanci ga sojojin kasar Amurka shi ne tsaron lafiyar rundunar sojojin kasar Amurka.Amma wasu mutanen kasar Amurka sun yi nuni da cewa,ba ma kawai gwamnatin kasar Amurka ba ta iya kyautata halin tsaron lafiya da kasar Iraki ke ciki ba,har ma ba ta iya tabbatar da tsaron lafiyar sojojin dake cikin sansaninta ba.Ana iya cewa,sojojin kasar Amurka dake zaune a kasar Iraki suna cikin hali mai hadari.
Na farko dai,`yan tawaye na kasar Iraki sun riga sun sami asirin sansanin sojojin kasar Amurka dake zaune a kasar Iraki.Saboda haka,ana tuhumar da mutanen kasar Iraki dake aiki a cikin sansanin sojojin kasar Amurka.Amma sansanonin sojojin kasar Amurka suna bukatar mutanen kasar Iraki da yawan gaske domin su yi aikin fassarawa da aikin gyarawa da aikin ginawa da aikin dafa abinci da sauransu.Wasu ma`aikatan rundunar sojojin kiyaye tsaron lafiya ta kasar Iraki su kan shiga sansanonin sojojin kasar Amurka.Shi ya sa akwai wuya a nemi mai kai hari daga cikinsu.
Na biyu,masu lura da al`amuran yau da kullum sun yi nuni da cewa,idan an kara karfafa aikin tsaron lafiyar sojojin kasar Amurka dake zaune a kasar Iraki,to,wannan zai sa albarkatai su kara raguwa.Ban da wannan kuma,idan an yi haka,to,wannan shi ma zai matsa lamba ga sojojin kasar Amurka.
Al`amarin Mosul ya auku ne kafin babban zaben da za a yi a karshen watan Janairu na shekara mai zuwa,ko shakka babu sojojin kasar Amurka za su kara kai farmaki ga `yan tawaye.
A ran 22 ga wata,a gun taron watsa labarai da ma`aikatar tsaron kasa ta kasar ta shirya,Mr.Donald Rumsfeld,ministan tsaron kasa na kasar Amurka ya bayyana cewa yana fatan za a kafa wata kasar Iraki mai zaman lafiya da dimokuradiya da kuma wadatuwa,amma a sa`i daya kuma,shi ma ya yarda da cewa dole ne a yi kokari. (Jamila Zhou)
|