Ran 16 ga wata, Hiroyuki Hosoda, shugaban ofishin majalisar ministocin kasar Japan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Japan ta yanke shawara a kan bai wa Li Denghui visa don shiga kasar Japan a shekarar nan, da kuma yarda da 'yan iyalinsa da su yi yawon shakatawa a garin Kanaza da na Kyoto na kasar Japan. Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin yana ganin cewa, wannan ya zama zugawa da goyon baya ne da kasar Japan ta yi wa 'yan a-ware na Taiwan da su jawo wa kasar Sin baraka, haka nan kuma ya zama kalubale ne ga babban sha'anin dinkuwar kasar Sin cikin lumana. Sa'an nan da babbar murya ne ya nemi gwamnatin kasar Japan da ta soke wannan shawara nan da nan.
Batun Taiwan yana da nasaba da harsashin siyasa na huldar da ke tsakanin Sin da Japan. A zamanin da, kasar Japan ta taba hadiye Taiwan da karfin soja kuma ta yi mulkin mallaka a Taiwan har cikin shekaru 50 da suka wuce. A cikin sanarwar da Sin da Japan suka bayar cikin hadin guiwarsu, a fili ne gwamnatin kasar Japan ta amince da Jamhuriyar Jama'ar Sin wadda ke wakiltar halalen gwamnatin Sin daya tak, ta nuna girmamawa da fahimta sosai ga matsayin kasar Sin a kan Taiwan wani kashi ne da ba a iya balle shi daga Jamhuriyar Jama'ar Sin. Wannan sanarwa ta daidaita batun matsayin Taiwan a fannin siyasa da shari'a, kuma ta tsaida ka'idoji da ake bi wajen daidaita batun Taiwan cikin gaskiya. Tsofaffin shugabannin kasar Japan sun taba bayyana a fili cewa, kasar Japan ba ta da kwadayi kan Taiwan ba.
Amma Hiroyuki Hosoda ya yi kururuwa cewa, a madadinsa ne, Li Denghui zai yi ziyara a kasar Japan, sabo da haka gwamnatin Japan ba ta da hujjar nuna kiyewa ba. Kalamin nan ba shi da tushe kuma maras kan gado ne. Sanin kowa ne, Li Denghui babban wakilin 'yan a-ware na Taiwan ne, kuma yana kawo lahani ga huldar da ke tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan kuma ga zaman lafiyar shiyya-shiyya. Tun bayan da Li Denghui da Chen Shuibian suka rike da hukumar Taiwan, sai hukumar Taiwan ta yi bakin kokari wajen neman abu na wai "'yancin kan Taiwan sannu a hankali" da "cire sunan kasar Sin", haka zalika sun yi nufin banza na neman balle Taiwan daga yankunan kasar Sin ta hanyar "yin kwaskwarima kan tsarin mulki" da ta shari'a. Dadin dadawa sun wuce iri da gona sun kago "Sin biyu" a duniya, da "Sin daya Taiwan daya", sun yi ta yin tarnaki da riciki ga huldar da ke tsakanin bangarori biyu na Zirin Taiwan. Ruwa a jallo Li Denghui ke neman samun damar yin ziyara a kasar Japan don neman samar da gurabe a kasashen waje ta yadda zai kara jawo wa kasar Sin baraka.
Kare mallakar kan kasa da cikakken yankinta babbar moriya ce ga kasar Sin. Batun Taiwan harkokin gida na kasar Sin ne, gwamnatin Sin da jama'arta sun dau niyyar tabbatar da dinkuwar kasar Sin gaba daya, kuma suna da karfi wajen cim ma burinsu.
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, manyan jami'an gwamnatin Japan sun yi ta yin shagali a haikalin Yusukuni don tunawa da manyan masu laifuffukan yaki a birnin Tokyo, wannan ya kawo babban lahani ga huldar siyasa da ke tsakanin Sin da Japan. Amma ga shi yanzu, gwamnatin kasar Japan ta sake tsolma hannu cikin harkokin gida na kasar Sin kan batun Taiwan, lalle ne wannan zai kara kawo lahani ga huldar da ke tsakanin kasashen nan biyu. Kamata ya yi, gwamnatin Japan ta sa kare huldar da ke tsakanin Sin da Japan a gaban kome, ta daidaita wannan batu yadda ya kamata, ta soke shawarar da ta yanke a kan amincewa da ziyarar da Li Denghui zai yi a kasar Japan. In ba haka ba, daga karshe, za ta debi kunya. (Halilu)
|