Ran 6 ga watan nan, a birnin Washington, Adam Ereli, mataimakin kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ya yi nuni da cewa, Amurka tana adawa da canja suna da yankin Taiwan za ta yi a hukumominta da ke ketare, kuma ta ki yarda da ko wane matakin da za a dauka a bangare daya wanda zai canja halin da ake ciki a zirin Taiwan.
Mista Ereli ya yi wannan furuci ne yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa kan yunkurin yankin Taiwan na canja sunayen hukumominta na ketare. Kuma yana mai cewar, kasar Amurka ba za ta baiwa yankin Taiwan goyon baya ba kan wannan batu. Kasar Amurka na fatan cewa, za a kiyaye kwanciyar hankali a zirin Taiwan. (Bello)
|