Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-11-18 20:22:56    
Kasar Sin ta nemi kasar Vanuatu da ta cika alkawarin da ta dauka mata game da batun Taiwan

cri
Ran 18 ga wata, Madan Zhang Qiyue, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing cewa, a tsanake kasar Sin ta nemi kasar Vanuatu da ta nuna biyayya ga ka'idoji da aka tsaida a cikin sanarwar kulla huldar diplomisiya tsakaninta da kasar Sin, kuma ta cika alkawari sosai da ta dauka wa kasar Sin dangane da batun Taiwan.

A gun taron ministoci na kasar Vanuatu da aka yi a ran 10 ga wata, an riga an yanke shawara a kan soke yarjejeniyar kulla huldar diplomasiya da firayim ministan kasar ta daddale a tsakaninta da hukumar Taiwan, sa'an nan gwamnatin Vanuatu ma ta bayar da sanarwa a kan wannan. Madan Zhang Qiyue ta yi wannan kalami yayin da take amsa tambayar da manema labaru suka yi mata. (Halilu)