Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-11-08 16:50:20    
Babban yankin kasar Sin bai taba tsoma baki kan musaye-musaye da hadin guiwar tattalin arziki da ake yi a tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan ba

cri
A ran 8 ga watan, direktan ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Mr. Chen Yunling ya ce, kodayake akwai bambancin matsayin siyasa a gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan, amma babban yankin kasar Sin bai taba tsoma baki kan musaye-musaye da hadin guiwar tattalin arziki da ake yi a tsakanin gabobin nan biyu ba.

Mr. Chen Yunling ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da kungiyar yin musayar sha'anin noma a tsakanin gabobi biyu ta Taiwan wadda ke karkashin Mr. Xu Xinliang, wato wani sanannen dan siyasa a Taiwan. Mr. Chen ya ce, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, babban yankin kasar Sin ya riga ya dauki matakai masu yawan gaske domin sa kaimi da nuna goyon baya ga hukumomin sha'anin noma na gabobin nan biyu da su yi hadin guiwa a tsakaninsu. Takwarorin hukumomin sha'anin noma na gabobin nan biyu ma sun kara yin musaye-musaye da cudanya a tsakaninsu kwarai. Ta hakan an samu sakamako da yawa daga wajen yin musaye-musaye da hadin guiwa a tsakanin gabobin nan biyu. (Sanusi Chen)