Ran 30 ga watan jiya, Mr Ghazi Al-Yawer, shugaban gwamnatin wucin gadi na kasar Iraki ya sauka kasar Kuwait don fara yin ziyara ta kwanaki 3 a kasar. Wannan karo na farko ne da shugaban kasar Iraki ya yi ziyara a kasar Kuwait har cikin shekaru 40 da suka wuce.
Mr Yawer ya sami maraba daga wajen Emir Sheikh Jaber na kasar Kuwait da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar. Bayan da ya sauka a kasar Kuwait, Mr Yawer ya yi jawabi a takaice, inda ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Kuwait da jama'arta saboda goyon baya da taimako da suka bai wa yakin Iraki don tumbuke mulkin Saddam Hussien, kuma ya nuna yabo ga kyakkyawar dangantakar aminci iri na 'yanuwa da ke kasancewa a tsakanin kasashensu biyu a cikin dogon lokaci. Sa'an nan ya jaddada cewa, hare-hare da aka tayar a kan kasar Kuwait a shekarar 1990 mataki ne da Saddam ya dauka shi da kansa, kuma ba su da nasaba da jama'ar kasar Iraki ba. Jama'ar kasar Iraki da ta Kuwait dukansu sun sha wahalhalu daga wajen danyen aiki da Saddam ya yi.
Ko da yake Iraki da Kuwait kasashe ne da ke makwabtaka da juna, amma shugaban kasar Iraki ya yi ziyarar karshe a kasar Kuwait ne a karshen shekarun 1960. Bayan da Jam'iyyar Baath ta Iraki da Saddam ya shugabanta ta sake rike da mulkin kasar a watan Yuli na shekarar 1968, shugaban kasar Iraki bai taba yin ziyara a kasar Kuwait ba. Sabili da haka wannan ziyarar da Mr Yawer ya yi tana da muhimmanci ga tarihi.
Masu lura da al'amuran yau da kullum sun nuna cewa, babban makasudin ziyarar da Mr Yawer ya yi a wannan gami shi ne, don neman kyautata huldar da aka lalata a tsakanin kasashen nan biyu sabo da hare-hare da kasar Iraki ta tayar a kan kasar Kuwait.
A watan Maris na shekarar 2003, sojojin taron dangi na Amurka da Britaniya sun tayar da yakin Iraki don neman tumbuke mulkin Saddam. Wannan ya sami goyon baya daga wajen kasar Kuwait. Bayan da Saddam ya sauka daga karagar mulkin kasa, an fara sassauta huldar da ke tsakanin kasar Iraki da ta Kuwait. Jami'an tsohuwar hukumar zartaswa ta wucin gadi ta Iraki da na gwamantin wucin gadi na yanzu bi da bi suka yi ziyara a kasar Kuwait, sun yi ta yin kokari wajen neman kyautata huldar da ke tsakanin kasashen nan biyu.
Manazarta suna ganin cewa, ziyarar nan ta Mr Yawer za ta aza harsashi ga maido da huldar tsakanin kasshen nan biyu daga duk fannoni, kuma an sa ran alheri cewa, za a kawar da sabane-sabane da ke kasancewa a tsakanin kasashen nan biyu.
Ya zuwa yanzu dai, ba a tabbatar da zaman karko a kasar Iraki ba, kuma ba a sami ci gaba da sauri wajen sake gina kasar Iraki ba. Ana bukatar mankudan kudade wajen sake yin manyan ayyukan kasa da aka lalata su a cikin yake-yake da aka yi har sau 3. Idan bangaren Kuwait ya nace ga neman kasar Iraki da ta biya mata diyyar yaki da yawanta ya kai dalar Amurka biliyan 160, to, ko shakka babu, za a kara karancin kudi wajen sake gina kasar Iraki. Sabo da haka wata babbar manufar ziyarar da Mr Yawe ya yi a kasar Kuwait ita ce don shawo kan shugabannin kasar Kuwai da su soke wannan diyyar yaki ko rage yawanta.
Bisa bincike da masu fadi a ji na yankin Gulf suka yi, an ce, ko da yake an riga an kyautata huldar siyasa da ke tsakanin kasar Iraki da ta Kuwait, kuma za a sami babban ci gaba wajen yin hadin guiwa tsakanin kasashen nan biyu a fannin tattalin arziki da fasaha ta wannan ziyarar da Mr Yawer ya yi a kasar Kuwait. Amma idan kasashen nan biyu sun kasa samun sakamako da ke gamsar da juna a kan matsalar biya diyyar yaki mai yawa ba, to, za a bukaci wani tsawon lokaci don mayar da huldar da ke tsakanin kasashen nan biyu yadda ya kamata a duk fannoni. (Halilu)
|