|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2004-09-23 20:34:24
|
Gwamnatin kasar Sin ta yi adawa da Amurka ta sayar da makamai ga Taiwan
cri
A gun taron manema labaran da aka shirya ran 23 ga wata a nan birnin Beijing,kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mista Kong Quan ya jadada cewa gwamnatin kasar Sin ta tsaya tam tam tana adawa da Amurka ta sayar da makamai ga Taiwan.
Mista Kong Quan ya ce sayar da makamai ga Taiwan da Amurka ta yi ya saba wa ka'idoji na dangantaka tsakanin kasa da kasa,da hadaddiyar sanarwa guda uku tsakanin kasar Sin da Amurka haka kuma ya saba manufar Sin daya da gwamnatocin Amurka da shugabanninta suka yi alkawarin binta da rashin goyon baya ga yancin kan Taiwan.Kasar Sin ta yi fatan Amurka za ta kiyaye alkawarinta kada ta ba da alamun kuskure ga kungiyoyin neman yancin kan Taiwan.(Ali)
|
|
|