Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-09-23 18:10:06    
Jami'ar Beijing Jami'a ce mai cikakkun sassan koyon ilmi daban daban masu fasaha da na kimiyya

cri

Jami'ar Beijing Jami'a ce mai cikakkun sassan koyon ilmi daban daban masu fasaha da na kimiyya, wadda tana da babban matsayin bincike ilmi sosai, wato tana shahara sosai a duk mafarin kasar Sin. A shekara ta l989 an kafa wannan jami'a, wato ita ce daya daga cikin manyan jami'a masu tsawon tarihi sosai na duk kasar Sin.

Bayan da wannan Jami'a ta sami bunkasuwa cikin shekaru dari da suka shige,yanzu, Jami'ar Beijing tana da sassan daban daban kamar na ilmin fasahohi da na zaman al'umma da na kimiyya da na aikin ba da labaru da sadarwa da na likitanci, Kuma tana da kolejoji 42, kuma cibiyoyin bincike nata sun kai 216, kuma tana da asibitoci masu koyarwa guda l8, daga cikinsu wadansu sassan koyo kaman na Sinansi da na Spain da na tarihi da na sauran ilmi suna shahara a duk kasar Sin.

Yanzu Jami'ar Beijing tana da dalibai masu neman digiri na farko guda fiye da dubu l5, yawan dalibai masu neman digiri na biyu da na matsayin docter sun kai dubu 12, Ban da haka kuma akwai dalibai da yawa na kasashen waje dake dalibta a wannan jami'a. Jami'ar nan tana da babban dakin karatu wanda ya fi girma a duk kasashen Asiya, Jimlar litattafan dake cikin wannan dakin karatu ta kai fiye da miliyan 6.29. In ka so kara neman sanin abubuwa na wannan jami'a sai ka shiga hanyar internet haka:http://www.pku.edu.cn/