Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-08-17 17:12:28    
Ministan harkokin waje na Australia ya sa kaimi ga Taiwan da kada ta ci gaba da neman samun 'yancin kai

cri

Ran 17 ga watan nan, Mr. Alexander Downer, ministan harkokin waje na Australia, wanda ke ziyara a kasar Sin, ya bukaci Taiwan da kada ta ci gaba da neman samun 'yancin kanta.

Mr. Downer ya yi wannan bayani ne a gun wani taron maneman labaru da aka yi a birnin Beijing. Ya ce, idan Taiwan ta ci gaba da neman 'yancin kanta, za ta kawo babban tangadi ga duk shiyyar da babban yankin kasar Sin da Taiwan ke ciki, musamman ma ga dangantakar da ke tsakanin su biyu. Shi kansa ya sake jaddada manufar da Australia ta tsaya a kan kullum watau kasar Sin 1 tak, lokacin da ya yi shawarwari tare da shugabannin kasar Sin.

Mr. Downer ya nuna cewa, daidaita batun Taiwan cikin lumana na bukatar lokaci, amma akwai yiwuwa. Ya kamata Australia da kasashen da batun ya shafa na wannan shiyyar da kungiyar Turai da Amurka, dukansu su sanarwa Taiwan a fili cewa, duk wani aikin da za a yi domin sanar da 'yancin kan Taiwan tsokana ce. (Bello)