Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-08-12 15:21:18    
Al'adar shan shayi ta mutanen kasar Sin

cri

    Masu karatu,kamar yadda kuka sani,tarihin shan shayi na mutanen kasar Sin ya riga ya kai fiye da shekaru dubu hudu,shayi shi ne abin sha da yawancin mutanen kasar Sin ke so.A nan kasar Sin,akwai wata karin magana,wadda ke bayyana cewa:A cikin zaman rayuwa na yau da kullkum na mutanen kasar Sin,abubuwa bakwai sun fi muhimmanci,wato su hada da: `ya`yan itace da shinkafa da man girki da gishiri da ruwan magin waken soya da ruwan tsami da kuma shayi.Daga nan,ana iya gane muhimamncin shayi dake cikin zaman rayuwar mutanen kasar Sin.A kasar Sin,mutane su kan shirya ruwan shayi ga baki domin su sha,wannan wata al`ada ce gare mu.Idan baki sun shiga kofa,sai mai gida ya ba su ruwan shayi cikin kwaf mai zafi,su sha tare su yi hira suna jin dadi.

    Al`adar shan shayi tana da dogon tarihi a kasar Sin.Mun ji an ce,kafin shekarar 280 bayan haihuwar Annabi Isa alaihissalam,a kudancin kasar Sin,akwai wata karamar kasa da ake kiranta `kasar Wu`,sarkin kasar yana so ya kira liyafa ga manyan jami`ansa kuma yana so ya ba su umurni cewar dole ne su sha giya har su bugu.Amma wani babban jami`I dake cikinsu mai suna Weizhao bai iya shan giya da yawa ba,shi ya sa sarkin ya yarda Weizhao ya sha shayi a maimakon giya.Bayan wannan,mutane sun fara shirya ruwan shayi ga baki.Ya zuwa daular Tang ta zamanin da,shan shayi ya riga ya zama wata al`ada ta mutanen kasar Sin.Mun ji an ce,wannan yana shafar addinin Buddha.Tun daga shekarar 713 AD har zuwa shekarar 741 AD,a wancan lokaci,mabiyan addinin Buddha su kan ji barci da yunwa saboda lokacin karanta littafin addinin Buddha ya yi tsawo sosai,shi ya sa wani tsohon mabiyan addinin Buddha ya shirya ruwan shayi domin su sha,to,shi ke nan sai ba su ji barci ba saboda ruwan shayi ta sa sun ji farin ciki.Daga nan,wannan al`ada ta yi ta yaduwa a wurare daban daban na kasar Sin.

    Ya zuwa shekarar 780 AD,masani mai yin nazari kan shayi na daular Tang Mr.Luyu ya takaita sakamakon da ya samu wajen dasa itacen shayi da dafa shayi da kuma shan shayi,kuma ya rubuta littafin shayi na farko na kasar Sin wato sunansa shi ne `littafin shayi`.Yanzu kowace shekara,wasu hukumomi ko kungiyoyi su kan shirya taron shan shayi domin taya murnar babban salla, alal misali,sabuwar shekara da sallar bazara ta gargajiyar kasar Sin da sauransu.

    A kasar Sin,shayi ya riga ya zama irin wani halin musamman na al`ada.Mutanen kasar Sin sun mayar da shan shayi a matsayin irin wata fasaha.Tun tuni har zuwa yanzu,a wurare daban daban na kasar Sin,an kafa ginin shan shayi iri daban daban,ana iya shan shayi ana iya dandana waina kuma ana iya kallon wasan fasaha a ciki.

    Shayi yana iri daban daban ne.Mutanen birnin Beijing suna so su sha shayi tare da furanni,mutanen birnin shanghai suna so su sha koren shayi,mutanen lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin suna so su sha jan shayi.

    Ban da wannan kuma,al`adun shan shayi na wurare daban daban na kasar Sin su ma sun sha banban,alal misali,a nan birnin Beijing,idan mai gida ya baiwa baki kofin ruwan shayi,kamata ya yi bako ya tashi tsaye nan da nan ya karbi kwafin ruwan shayi da hannu biyu kuma ya ce,`Na gode.`A lardin Guangdong da lardin Guangxi na kudancin kasar Sin,baki ya kan kwankwasa tebur da yatsu na hannun dama sau uku,nufinsa shi ne nuna godiyarsa.