Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2004-08-11 18:04:42    
Shugaban babbar kungiyar sa kaimi ga hade kasar Sin cikin lumana ta Brazil ya ce manufar kasa daya tsarin mulki iri biyu ya dace da moriyar 'yan uwammu na Taiwan.

cri

Ran 11 ga watan nan, a nan birnin Beijing, Mr. Zhang Wuji, shugaban babbar kungiyar sa kaimi ga hade kasar Sin cikin lumana ta Brazil ya ce, "hade kasar Sin cikin lumana " da "kasa daya tsarin mulki iri biyu" hanya ce mafi kyau da ake bi wajen neman daidaita maganar Taiwan yadda ya kamata, ta dace da moriyar dukan Sinawa, kuma ta dace da moriyar 'yan uwammu na Taiwan.

Mr. Zhang yana ganin cewa, manufar kasa daya tsarin mulki iri biyu ta yi la'akari da tarihi da halin da ake ciki yanzu a Taiwan sosai. Bisa manufar nan, ba ma kawai 'yan uwammu na Taiwan za su ci gaba da yin irin zaman rayuwa da suka saba, za su more dimokuradiya da 'yanci ba, hatta ma za su sami 'yanci mai fi yawa, su more arziki da wadata na kasar mahaifarsu.(Bello)