
Ran 19 ga wata, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mista Wu Bangguo ya nanata a nan birnin Beijing cewa, ko kusa, kasar Sin ba za ta yarda da duk wanda zai balle Taiwan daga yankunan kasar ta ko wace hanya ba.
Mista Wu Bangguo ya yi wannan furuci ne yayin da yake ganawa da Hormando Vaca Diez, shugban majalisar dokoki ta kasar Bolivia kuma shugaban majalisar datijai ta kasar. Mista Wu Bangguo ya kara da cewa, ya kansace da kasar Sin daya tak a duniya, Taiwan wani kashi ne da ba za a iya balle shi daga yankunan kasar Sin ba. Wannan ya tabbatar a da da yanzu, kuma ra'ayi daya ne ga kasashe dabam daban. Ya kuma nuna yabo ga kasar Bolivia bisa manufarta game da kasar Sin daya tak a duniya. (Halilu)
|