Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2003-09-30 23:24:13    
Rediyon kasar Sin

cri

    An kafa Rediyon kasar Sin wato China Radio International a ran 3 ga watan Disamba na shekarar 1941. Yanzu yana watsa shirye-shirye a kullum cikin harsuna 43 ga wurare daban-daban a duk fadin Duniya.  Harshen Hausa shi ne daya daga cikinsu.

    Ran 28 ga watan 5 na shekarar 1997 ne muka fara aiki a cikin sabon ginin da ke yammancin birnin Beijing na kasar Sin. Kafin wannan lokaci kuwa, mun yi aiki a cikin babban ginin ma'aikatar watsa labarai da TV da sinima dake tsakiyar birnin Beijing.

    Sabon ginin nan shi ne ginin watsa labarai zuwa kasashen duniya mafi ci gaba a duniya. Fadinsa ya kai muraba'in mita fiye da dubu hamsin. Gaba daya, yana da hawa 15. An sayi dukkan injuna ba da dadewa ba, dukkansu sabbin kayayyaki ne, kuma sun fi kyau a duniya.

    A cikin ginin, ban da ofisoshi da dakunan daukan murya, akwai dakin karatu da dakin cin abinci da shan kofi da dai sauransu. Muna da wani muhallin aiki mai kyau. Idan kuna da lokaci, sai ku zo ku yi ziyara a nan, za mu yi muku maraba sosai.

    Cikakken adireshinmu:

    Sashen Hausa

    China Radio International

    Beijing 100040

    China

    Adireshin Akwatin Gidan Wayan Rediyon Kasar Sin a Lagos na Nijerya:

    Sashen Hausa

    China Radio International

    P.O.Box 72100

    Victoria Island

    Lagos

    Nijeriya.